Isa ga babban shafi
Iraq

Baghdadi na Iraqi ya fito a Bidiyo

Shugaban sabuwar kasar Daular Islama a Iraqi Abu Bakr al Baghdadi ya yi kira ga dukkanin al’ummar musulmi su yi masa biyayya a cikin wani sakon bidiyo da ya aiko. Kamfanin Dillacin Labaran Faransa ya ruwaito cewa Baghdadi ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke gabatar da hudubar Juma’a a birnin Mosul da ke arewacin Iraqi.

Abou Bakr al-Baghdadi, Shugaban Mayakan ISIS da suka kafa sabuwar Daular Islama a Iraqi
Abou Bakr al-Baghdadi, Shugaban Mayakan ISIS da suka kafa sabuwar Daular Islama a Iraqi AFP PHOTO / HO /US Department of State
Talla

A ranar 29 ga watan Yuni ne Baghdadi ya ayyana kafa sabuwar daular Islama a yankunan da Mayakan ISIL suka mamaye na kasashen Iraqi da Syria.

Baghdadi ya fito ne sanye da bakin rawani yana yin kira ga mabiyansa akan su yi masa biyayya tare neman gyra idan ya yi kuskure a matsayin shi na shugaba.

Wannan shi ne dai karon farko da Baghdadi ya nuna kansa tun lokacin da ya ke gwagwarmaya a Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.