Iraqi-Amurka
Amurka ta yi watsi da bukatar Kurdawan Iraqi
Kasar Amurka ta yi watsi da bukatar da shugaban gwamnatin cin gashin kai ta Kudurwan kasar Iraki Massud Barzani ya gabatar wa majalisar dokokin yankin Kurdistan, inda ya bukaci a amince a shirya kuri’ar jin ra’ayin jama’a domin ballewar yankin daga kasar baki daya.
Wallafawa ranar:
Talla
Mai Magana da yawun fadar Amurka ta White House Joseph Earnest, ya ce babu yadda Iraqi za ta iya tunkarar Mayakan jihadi face idan kasar na hade.
Firaministan Iraqi Nuri al-Maliki ya yi tayin afuwa ga Mayakan da suka karbe ikon wasu biranen kasar, tare da yin watsi da bukatar Barzani.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu