Isa ga babban shafi
Iraqi-Turkiya

Turkiyya na kokarin kwato 'yan kasar da aka sace a Iraki

Hukumomi a kasra Turkiya sun bayyana aniyar tattaunawa da masu tada kayar baya na yankin Arewacin Iraqi da ke ci gaba da yin garkuwa da ‘yan kasar.Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatocin kasashen duniya ke kiraye kirayen neman a tabbatar an kwato mutanen daga hannun masu garkuwa da su.Wani babban jami’in gwamnatin kasar ta Turkiyya, da bai so a bayyana sunan shi ba, yace sun karfafa matakan sun a diplomasiyya, don ganin an sami nasarar ceto mutanen da aka sace.A ranar laraba da ta gabata ‘yan bindiga, na kungiyar ISIL suka yi awon gaba da mutane 49 a daga ofishin jakadancin kasar Turkiyya a birnin Monsul, cikin wadanda aka sace harda jakadan kasar ta Turkiyya.‘Yan kungiyar ta ISIL sun kuma sace wasu drebobin motocin kasar ta Turkiyya, da ke aiki a wata cibiyar wutar lantarki a birnin na Mosul.Sai dai tuni hukumomin birnin Ankara suka sha alwashin daukar fansa, in har ‘yan bindigar suka illata ‘yan mutanen, tare da kira ga ‘yan kasar da ke Iraki su gaggata Ficewa. 

Shugaban kasar Turkiya, Tayyip Erdogan
Shugaban kasar Turkiya, Tayyip Erdogan REUTERS/Umit Bektas
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.