Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Amurka na nazarin taimakawa Iraqi

Kasar Amurka ta sha alwashin bai wa shugabanin kasar Iraqi duk taimakon da suke bukata don murkushe ma su tada kayar bayan da ke ci gaba da kwace garuruwa daga hannun jami’an gwamnati. Kakakin fadar White House, Jay Carney, yace Amurka ta yi Allah wadai da hare haren da Mayakan Jihadi ke kai wa da niyyar kafa kasar Islama.

Jami'an tsaron Iraqi sun fice sansaninsu bayan Kurdawa sun karbe ikon Kirkuk
Jami'an tsaron Iraqi sun fice sansaninsu bayan Kurdawa sun karbe ikon Kirkuk REUTERs
Talla

Carney yace bukatar su shi ne ganin ‘Yan kasar Iraqi sun hada kansu don gina kasa.

Rahotanni daga Iraqi sun ce Mayakan na Jihadi sun karbe ikon garin Kirkuk da yankin arewacin Nineveh da kudancin Salaheddin.

Yanzu haka kuma sun doshi Bagadaza bayan sun karbe ikon Dhuluiyah, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Faransa ya ruwaito.

Mayakan sun kunshi ‘Yan sunni da ke neman karya gwamnatin Shi’a da ke mulki a Iraqi.
Mai magana da yawun kungiyar Abu Mahammed al-Adnani, yace zasu kwace ikon Bagadaza babban birnin kasar da kuma Karbala yankin mabiyaya Shi’a.

Kasar Amurka tana nazarin yin amfani da kuramen jiragen yaki masu tuka kansu don taimakawa kasar Iraqi, wannan kuma na iya sa Amurka ta dawo Iraqi bayan ta fice a 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.