Isa ga babban shafi
Iraqi

Masu tada Kayar baya a Iraqi sun kama Garuruwa 6 na yankin Kirkuk

Mayakan jihadin kasar Iraqi sun kama Garuruwa 6 da ke yankin Kirkuk, bayan da a jiya Talata suka kama Garin Ninive da ke yankin Arewacin kasar, kamar yadda majiyoyin ‘yan sanda suka tabbatar

japantimes.co.jp
Talla

Mayakan dai sun samu nasarar kama garin Hawija da kuma wasu kananan Garuruwa masu makwabtaka da shi irin su Zab, Riyadh da Abbasi, da ke yammacin Kirkouk, babban birnin yankin na kirkuk. Bugu-da-kari Garuruwan Rashad da Yankaja da ke kudanci sun fada hannun mayakan, kamar yadda Kanal Ahmed Taha na rundunar sojan kasar ta Iraqi ya sanar.

Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa, ‘yan sanda da Sojoji sun zubar da makamansu sun tsere daga garin Zab.

Dan majalisar mashawartan yankin Hawija, Hussein al-Joubouri, ya ce yana ganin Dakarun na gwamnati sun samu umarnin bari garin ne, al’amarin da ya baiwa ‘yan tsageran damar kama garin tare da kafa Tutarsu a ciki.

Kasar Amurka a ta bakin kakakin ma’aikatar harakokin wajenta Jennifer Psaki, ta bayyana mayakan jahadin da zama babbar barazana ga daukacin yankin.

Shima dai babban Sakataren Majalisar dunkin Duniya Ban Ki-moon ya nuna matukar kaduwarsa da kama garin Mossoul, garin na 2 mafi girma a Iraki da mayakan jahadin suka yi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.