Isa ga babban shafi
Syria

Dakarun Syria sun karbe ikon wasu yankunan Damascus daga hannun ‘Yan tawaye

Dakarun Gwamnatin Bashar Assad sun fatattaki rundunar ‘Yan Tawaye daga wasu yankunan birnin Damascus, mako guda bayan ‘Yan Tawayen sun kaddamar da yaki a babban birnin kasar. yanzu haka ana ci gaba da gwabza yaki a hedikwatar Jami’an tsaro a birnin Aleppo.

Wani Harin Bom da aka kai a birnin Damascus na kasar Syria
Wani Harin Bom da aka kai a birnin Damascus na kasar Syria Reuters
Talla

‘Yan rajin tabbatar da Demokradiya masu adawa da Gwamnatin Assad sun tabbatar da karbe ikon yankin Mezzah a Damascus tare da bayyana cewa dakarun Gwamnati sun kashe farin kaya mutane 20 da suke zargin sun taimakawa ‘Yan Tawaye.

Dakarun Gwamnati sun kaddamar da yaki ne domin daukar fansar kisan wasu manyan Jami’an gwamnatin Assad da ‘Yan tawaye suka kashe a wani harin Bom da aka kai a ranar Larabar makon jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.