Isa ga babban shafi
Syria

Sabon rikici ya barke a Syria

A wayewar garin yau Laraba, an ga bakin hayaki ya turnike saman birnin Damascus a yayin da wani sabon fada ya barke tsakanin ‘Yan tawaye da dakarun Gwamnatin shugaba Bashar al- Assad. Wata kungiyar da ke shirya tsara borin da ‘Yan tawayen ke yi da ake kira Local Coordination Committee (LCC) ta fadawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa an kai hare-hare a yankuna daban daban na garin, ta kuma kara da cewa hare-haren da aka kai kan yankin Qaboon ya murkushe yankin.   

Hayaki ya turnike wani yankin kasar Syria
Hayaki ya turnike wani yankin kasar Syria AFP
Talla

Haka kuma ababuwan hawa kadan ne a ke gani a garin a yayin da ‘Yan tawayen su ka bayyana cewa sun fara wani sabon harin da su ka yi wa lakabi da “Girgizar kasar Damascus a Syria” wanda zai ceci kasar Syria daga dakarun gwamnati
Bangarorin biyu, na Free Syrian Army da dakarun gwamnati su ka yi wata arangama a sanyin safiyar yau a yankunan Al –Midan da gundumar Zahira da kuma Kudancin garin Assali.
 

Rahotan LCC ya kara da cewa an jiyo harbe -harbe da kuma tashin bama bamai a yammacin yankin Mashrou- Dumar.
Haka kuma an ji harbe-harbe a yankin Jdaidet Artu duk a cikin garin na Damascus inda wutan lantarki ta dauke saboda arangamar, a yayin da dakarun gwamnati su ka kuma kai hari garin Zabadani da ke da iyaka da kasar Lebanon.

Kungiya kare hakkin Bil’ Adama mai suna Syrian Observatory for Human Rights ta ce an yi mafani da manyan makamai wajen kai hare-hare akan yankunan Tal Kalah, da Khsaldiyeh da Qarabis da kuma Juret al- Shiyah duk a garin Homs.
 

‘Yan tawayen kasar ta Syria a ajiya ne su ka bayyana cewa yakin samar ma kasar Syria ‘yanci yanzu ya fara.
 

Kungiyar kare hakkin Bil Adaman ta kara da cewa akalla mutane 93 aka kashe a sabon rikicin da ya barke a jiya Talata cikinsu harda fareren hula 48.
 

A yayin da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da wani taro a yau don daukan sabon matakin da zai kawo karshen rikicin na Syria, kasar Rasha ta ki canza matsayinta akan batun
 

Shugaban kasar ta Rasha Vladimin Putin ya ki yarda a yi amfani da karfin soji don kawo karshen rikicin, a yayin da kasar Amurka da kawayente ke so a yi hakan.
Kwamitin na ta kokarin hada kawunan mambobi sa wanda yin hakan zai nunawa kasar ta Syria cewa za a dauki wani mataki.
 

Wakili na musamman da MDD da kasashen larabawa su ka nada, Kofi Annan, ya ziyarci kasar Syria ya kuma tattauna da shugaba Putin.
A ganawar da ya yi da ‘Yan jarida Annan, ya ce tattaunawarsu da Putin ta karkata ne kan yadda za a kawo karshen rikicin na Syria da kuma yadda za a samar da gwamnatin wucin gadi.
 

A ranar Juma’a mai zuwa ne, wa’adin kwanaki 90 da aka ba tawagar mutane 300 MDD ta tura don saka ido akan rikicin na Syria da kuma tabbatar da tsagaita wuta zai kare.
Kwamitin tsaron ne ke da alhaki ya kara yawan kwanakin.
 

Tuni dai kasar Amurka da kawayenta su ka ce rashin aiwatar da tsare tsaren nan guda shida da Annan ya fitar da kuma ganin yadda rikicin ke kara tsamari ya sa ya zama dole a yi hukunci akai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.