Isa ga babban shafi
Syria

Wa’adin tawagar MDD ya kare a yayin da rikicin Syria ke kara tsamari

A yau ne tawagar masu zura ido na Majalisar dinkin duniya a kasar Syriya za ta kawo karshen wa’adin aikin da aka diba mata,A jiya Alhamis wani babban jami’in sojan Majalisar ya isa a birnin Damas na kasar ta Syria domin karbar aiki daga shugaban tawagar Janar Robert Mood 

Wakilin MDD da kasashen larabawa na musamman akan rikicin Syria, Kofi Annan
Wakilin MDD da kasashen larabawa na musamman akan rikicin Syria, Kofi Annan Reuters/路透社
Talla

Kasar Birtaniya ta nemi kara wa’adin tawagar da kwanaki 30 a yayin da kasar Pakistan ta nemi karin wa’adin kwanaki 45.

Wani Jami’in kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya ce mai yiwa tawagar ta fice a gurguje daga kasar ta Syria ganin yadda rikicin ke kara tsamari wanda hakan ba zai bada da dama kara ma tawagar wa’adi ba.

An tura tawagar mai dauke da sojoji 300 wanda basa dauke da makamai tare da fararen hula 100 kasar Syria domin su tabbatar da tsagaita wuta tsakanin dakarun gwamnati da 'Yan tawayen  domin kawo karshen rikicin na Syria.

Hakan kuma yarjejeniya ce tsakanin wakilin MDD da kasashen larabawa su ka saka na musammam, Kofi Annan da shugaba Bashar al- Assad.

Tawagar ta kuma janye daga ayyukan da ta ke gudanarwa a watan Yunin da ya gabata ganin yadda harkar tsaro ke kara tabarbrewa a kasar.

Kasashen Rasha da China sun hau kujerar na ki akan aka kara wasu tankunkumi akan tura tawagar ta MDD a yayin da kasashen Turai da kasar Amurka ke so a yi hakan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.