Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Ana amfani da Yara kanana a matsayin garkuwar yaki a Syria, inji MDD

A wani Rahoton Majalisar Dinkin Duniya game da rikicin Syria, an bayyana cewa dakarun gwamnati suna gallazawa yara kanana tare da amfani dasu a matsayin garkuwar yaki a lokacin da suke musayar wuta da ‘Yan tawaye. Rahoton yace kimanin yara kanana 1,200 suka mutu watanni 15 da aka kwashe ana zanga-zangar adawa da Bashar al Assad.

Wasu bama bamai da aka kai a Al Qusoor a birnin Homs
Wasu bama bamai da aka kai a Al Qusoor a birnin Homs REUTERS/Waseem Al Qussoor
Talla

Rahoton yace Makarantu sun koma cibiyar gallazawa yara kuma ana amfani da makarantun a matsayin sansanin Soji.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya bukaci hukumomin Syria, bayar da dama ga masu sa ido domin shiga birnin Al Heffa, inda dakarun Gwamnati ke yin ruwan wuta. A cewar Ban Ki-moon matakan soja da hukumomin Syria ke dauka, wajen harba makamai daga jiragen sama ya yi sanadiyar raunata fararen hula da dama.

Hukumar kare hakkin Bil’adama ta Human Rights Watch ta yi kira ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kakabawa kasar Syria takunkumi da ya hada da takunkumin haramta shigo da makamai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.