Isa ga babban shafi

Bangaren adawa ya yi watsi da sabon kundin tsarin mulkin Togo

Bangaren adawa a Togo ya yi watsi da sabon kundin tsarin mulkin kasar da majalisa ta amince da shi da zai sauya salon mulkin kasar daga tsarin shugaban mai cikakken iko zuwa Firaminista.

Shugaba Faure Gnassingbé na Togo.
Shugaba Faure Gnassingbé na Togo. © AP/Gbemiga Olamikan
Talla

Bangaren adawar ya bayyana matakin a matsayin wani yunkuri da zai kawar da shirin zaben shugaban kasar da ke tafe baya ga kara wa’adin mulkin shugaba Faure Gnassingbe.

Yanzu haka dai ana dakon sa-hannun shugaban kasa gabanin mayar da kudirin sauyin kundin tsarin mulkin zuwa doka bayan da majalisar ta aminta da kudirin cikin makon nan.

Karkashin sabon kundin tsarin mulkin wanda bangaren adawar ke kalubalanta na nufin kai-tsaye kasar za ta koma zaben ‘yan majalisa ne wadanda daga cikinsu za a rika fitar da Firaminista.

A shekarar 2025 ne wa’adin shugaba Gnassingbe ke shirin kawo karshe, matakin da zai bayar da damar kiran sabon zaben shugaban kasa karkashin kundin tsarin da yanzu haka kasar ke amfani da shi.

Kwararru a bangaren shari’a na ganin sabon kundin tsarin mulkin zai kange matsalar wa’adi mai yawa da ‘yan takara kan nema wajen shugabancin kasar.

Majalisar wadda ke tafiya ba tare da bangaren adawa ba, tun farko 'yan adawar sun kaurace wa zaben 'yan majalisa na shekarar 2018 da ya kai ga kafa majalisar ba tare da hamayya ba, dalilin da ake ganin shi ya kai ga nasarar amincewa da sabunta kundin tsarin mulkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.