Isa ga babban shafi
Togo - Siyasa

Gwamnatin Togo na shan matsin lamba kan tsare tsohon ministan sadarwa

Jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula a kasar Togo, sun bukaci gwamnati ta saki tsohon ministan sadarwa Djimon Ore dake shugabancin Jam’iyyar FPD da aka kama a makon jiya ba tare gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Tsohon ministan sadarwa Djimon Ore dake shugabancin Jam’iyyar FPD
Tsohon ministan sadarwa Djimon Ore dake shugabancin Jam’iyyar FPD © Icilome.com
Talla

Ya zuwa yanzu dai babu wani zargi da aka gabatar akansa, amma kuma rahotanni sun ce ana tuhumarsa ne da yin kalaman batanci saboda sukar da ya yiwa shugaban kasa Faure Gnassingbe da mahaifinsa a lokacin bikin cika shekaru 61 da samun ‘yancin kan kasar.

Ore ya ce adadin zubar da jinin da Togo ta gani sakamakon mulkin kama karyar iyalan gidan Gnassingbe ya zarce kisan kare dangin da aka yi a kasar Rwanda.

Majiyar ta kuma ce ana zargin Ore da yunkurin tunzura jama’a domin gudanar da bore da kuma tada hankali.

Jam’iyyar ANC tace Ore yayi amfani da damar sa ta fadin albarkacin baki ne, kuma hakan bai sabawa kundin tsarin mulkin kasa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.