Isa ga babban shafi
Togo

Shugaba Faure Gnassingbe ya nada mace Firaministar Togo karon farko

Shugaban Togo Faure Gnassingbe ya nada Victoire Tomegah Dogbe a matsayin mace ta farko da za ta rike mukamin Firaminista a kasar domin maye gurbin Komi Selom Klassou.

Shugaba Faure Gnassingbé, na Togo.
Shugaba Faure Gnassingbé, na Togo. PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Dogbe mai shekaru 60 ta hannun daman shugaba Gnassingbe ce, kuma tun daga shekarar 2009 ta ke rike da mukamin babban hafsa a fadar sa.

Tun bayan rantsar da shugaban kasa a watan Fabarairu domin yin wa’adi na 4 ake saran zai yi wa gwamnatin kasar garambawul, amma annobar korona ta dakatar da shirin.

Gnassingbe ya yi takarar wa’adi na 4 ne bayan sauya kundin tsarin mulki, domin ganin iyalan gidan su sun cigaba da mulki tun daga lokacin da kasar ta samu 'yanci.

Nasarar shugaban ta haifar da zanga zangar 'yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.