Isa ga babban shafi
Afrika

Firaministan Togo yayi murabus

Firaministan Togo Komi Selom Klassou ya mika takardar murabus din sa da gwamnatin ministoci dake aiki a karkashin sa kamar dai yada fadar Shugaban kasar ta sanar a jiya juma’a.

Komi Selom Klassou ,Tsohon Firaministan kasar Togo
Komi Selom Klassou ,Tsohon Firaministan kasar Togo RFI hausa
Talla

Nan take Shugaban kasar Faure Gnassingbe ya yi na’am da wannan bukata,tareda yaba masa ganin irin jan kokarin da yayi wajen bunkasa tattalin arzikin kasar ta Togo a dan tsakanin nan duk da cewa akwai yan matsalloli dake hanna ruwa gudu.

Ana dakon Shugaban kasar tun bayan lashe zaben watan fabrairu ,ya aiwatar da sauye-sauye ta fanin shugabanci duk da fuskanatr bore daga bangaren yan adawa,sai dai hakan ba ta samu ba sabili da cutar Coronavirus.

Shugaban kasar Faure Gnassingbe da ya gaji mahaifin sa da ya shugabanci kasar tsawon shekaru 38,ya dahe kan karagar mulkin kasar ne a shekara ta 2005,yayinda tsohon Firaminista Komi Selom Klassou ya jagoranci gwamnatin kasar tun a shekara ta 2015 kafin daga bisali ya mika takardar murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.