Isa ga babban shafi
Togo

Jami'an tsaro sun sallami jagoran 'yan adawar Togo

Bayan share tsawon kwanaki uku a tsare, jami’an tsaron Togo sun sallami jagoran ‘yan adawar kasar Agbeyome Kodjo da wasu mukarranbansa a cikin daren jiya.

Agbéyomé Kodjo cikin wata rumfar zabe a birnin Lomé, ranar 22 ga watan fabarairun 2020.
Agbéyomé Kodjo cikin wata rumfar zabe a birnin Lomé, ranar 22 ga watan fabarairun 2020. REUTERS/Luc Gnago
Talla

Hukumar tara bayanan sirrin kasar wadda ta tsare shi tsawon wadannan kwanaki, ta ce daga yanzu an mika lamurran dan adawar a hannun ma’aikatar shari’a, wadda ta gindaya masa sharuda ciki har da zaunawa ba tare da fita daga kasar ba, sannan kuma dole ya daina ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben shugabancin kasar da aka yi cikin watan fabarairun da ya gabata.

Bayan kammala zaben watan fabarairu, duk da cewa shugaba Faure Gnasingbe ne ya yi nasara, amma Kodjo ya yi watsi da sakamakon, tare bayyana kansa a matsayin zababben shugaban kasar Togo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.