Isa ga babban shafi

Gwamnatin Togo ta dakile shirin 'yan adawa na yin zanga-zanga a Lome

Gwamnatin Togo ta haramta wani gangamin ‘yan adawa da aka shirya yi yau Asabar a Lome, babban birnin kasar saboda dalilai na tsaro.

'Yan sandan kasar Togo yayin sintirin dakile zanga-zanga a birnin Lomé a shekarar 2017.
'Yan sandan kasar Togo yayin sintirin dakile zanga-zanga a birnin Lomé a shekarar 2017. YANICK FOLLY / AFP
Talla

Sai dai yayin martani kan matakin, kawancen ‘yan adawa a kasar ta Togo, ya sha alwashin ba zai janye aniyarsa ba, inda ya dage gudanar da zanga-zangar zuwa wata mai zuwa.

Kawancen ‘yan adawar da aka fi sani da DMK a takaice, wanda ya kunshi jam'iyyu bakwai da kungiyoyin farar hula da dama, ya shirya gudanar da zanga-zangar ne domin nuna adawa da tsadar rayuwa, da rashin shugabanci nagari.

Ba kasafai dai ake gudanar da gangamin 'yan adawa a Togo ba inda ‘yan adawa suka ce an yi wa 'yan adawa shakar mutuwa a karkashin Shugaba Faure Gnassingbe, wanda ya shafe shekaru 17 yana mulkin kasar.

Wannan dai shi ne karon farko da mahukuntan Togo suka haramta gangamin 'yan adawa a baya bayan nan saboda dalilai na tsaro. Tun bayan makamancin matakin da suka dauka a yayin fama da annobar Korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.