Isa ga babban shafi

Libya ta kori bakin haure sama da 200 zuwa kasashen Nijar da Chadi

NIJAR – Hukumomi a kasar Libya sun ce, an fara shirin mayar da bakin haure 28 zuwa kasashen nijar da kuma Chadi, a wani aikin hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya ta bullo da shi.

Wasu bakin haure da ke zaune a a wata cibiyar bayar da agajin gaggawa dda ke tsibirin Lampedusa na kasar Italiya, ranar 15 ga watan Satumba, 2023.
Wasu bakin haure da ke zaune a a wata cibiyar bayar da agajin gaggawa dda ke tsibirin Lampedusa na kasar Italiya, ranar 15 ga watan Satumba, 2023. AP - Cecilia Fabiano
Talla

Hukumar da ke yaki da fataucin bil adama a Libya, ta ce bakin haure 120 ‘yar kasar Nijar ne suka dauki hanyar zuwa Yamai daga Libya, yayin aikin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin kasar da hukumar kula da kaura ta Majalisar Dinkin Duniya IOM.

A cewar hukumomin gwamnatin Libya da ke zama a gabashin kasar, yanzu haka za a tura bakin hautre 128 zuwa kan iyakar Chadi.

Tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaba, Moamer Kadhafi a shekarar 2011, aka samu rarrabuwar kawuna a kasar Libya, inda a yanzu ake da gwamnati biyu a kasar, wato a gasbhi da kuma yammaci.

Kasar da ke arewacin Afirka ta kasance wurin yada zangon dubban bakin haure da ke neman tsallakawa zuwa Turai ta ruwa a kowacce shekara, inda suke fadawa hannun masu safarar mutane.

Moussa al-Koni, shine mataimakin shugaban kasar, yayin wani taron manema labarai yawancin bakin hauren da ake kamawa sun fito ne daga kasashen Nijar da kuma Chadi.

A cewar IOM, sama da bakin haure 700,000 yawancin su ‘yan kasashen Masar da kuma Nijar ne suka shiga Libya daga wata Mayun zuwa watan Yunin 2023.

A ranar Litinin ne, ministan cikin gida na kasar Libya, Imed Trabelsi ya gana da wakilin IOM a nahiyar Afirka, Othman Belbeisi kan yadda za a kawo karshen matsalar kwararar bakin haure a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.