Isa ga babban shafi

Gwamnatin Chadi ta musanta ikirarin 'yan tawayen kasar na kashe mata sojoji

Gwamnatin Chadi ta musanta labarin kisan sojojin kasar 10 da ake zargin mayakan tawaye da kaiwa sojojin harin da ya yi sanadin mutuwar su a yankin arewacin kasar.

Yankin na Tibesti dai na cikin yankunan da ke shan fama da hare-haren ‘yan tawaye a Chadi
Yankin na Tibesti dai na cikin yankunan da ke shan fama da hare-haren ‘yan tawaye a Chadi AFP - AURELIE BAZZARA-KIBANGULA
Talla

Guda daga cikin kwamandojojin dakarun kasar ne ya musanta zargin kisan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce tabbas mayakan tawayen sun kaiwa sansanin sojojin hari a kauyen Wouri da ke yankin Tibesti na arewacin kasar, mai iyakan da Niger da Libya, amma ba a hallaka adadin sojojin ba.

Kungiyar tawayen da ake zargi da kisan dai na cikin wadanda suka ki amincewa su shiga yarjejeniyar sulhu da gwamnatin sojin kasar, kuma tuni ta yi ikirarin hallaka sojojin 10, tare da garkuwa da karin guda 8.

Ko da yake karin bayani kan batun kakakin gwamnatin sojin Chadin, Abderaman Koulamallah ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP  cewa mayakan tawayen su 20 sun kustsa kauyen kan babura, kuma sun kai hare-hare amma batun kisan sojojin farfaganda ce kawai.

Yankin na Tibesti dai na cikin yankunan da ke shan fama da hare-haren ‘yan tawaye a Chadi, tun da kasar ta sami ‘yancin kanta daga Faransa a 1960.

Amma dai lamarin harin ya fi kamari daga 2012 zuwa yanzu bayan da aka gano albarkacin danyen gwal shimfide a karkashin kasa, abinda ake ganin ‘yan tawayen kasar da na Sudan na sacewa don daukar nauyin ta’addancin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.