Isa ga babban shafi

An saki Ahmed Douma mai fafutuka a Masar bayan afuwar shugaban kasar

Dan kasar Masar Ahmed Douma, wanda ya kasance jigo a rikicin kasar a shekarar 2011, wanda ya shafe shekaru 10 a gidan yari, an sake shi bayan afuwar da shugaban kasar ya yi, a cewar lauyoyinsa a yau asabar.

Abdel Fattah al-Sissi Shugaban Masar
Abdel Fattah al-Sissi Shugaban Masar © AFP
Talla

Labarin da lauya Tarek Elawady, mamba a kwamitin afuwar shugaban kasar ya sheidawa manema labarai. Fitaccen lauyan nan mai fafutukar kare hakkin bil adama Khaled Ali da wasu masu fafutuka daga baya sun saka hoton Douma da ya bar gidan yarin na Badar a wajen birnin Alkahira, wurin da aka sha suka kan rashin kyawun yanayi.

Mai rajin kare hakokin bil Adam a Masar Douma
Mai rajin kare hakokin bil Adam a Masar Douma REUTERS/Al Youm Al Saabi Newspaper

Idan aka yi tuni an yankewa Douma hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari a shekarar 2015 bisa samunsa da laifin yin artabu da jami'an tsaro,aka kuma yanke masa hukuncin daurin shekaru 15 a shekarar 2019. A cikin wannan shekarar, babbar kotun daukaka kara ta Masar ta amince da rage hukuncin da aka yanke, da kuma tarar Fam Masar miliyan shida (dala 372,000 a lokacin). Douma, mai shekaru 37 a duniya, ya kasance babban mai fafutuka a rikicin da ya barke a shekara ta 2011 da ya hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak da ya dade yana mulkin kasar.

Tsohon mataimakin Shugaban kasar Hosni Moubarak kuma tsohon Shugaban Masar  da Anouar el-Sadate tsohon Shugaban Masar a ranar  6 ga watan Oktoba na 1981
Tsohon mataimakin Shugaban kasar Hosni Moubarak kuma tsohon Shugaban Masar da Anouar el-Sadate tsohon Shugaban Masar a ranar 6 ga watan Oktoba na 1981 © AFP

An kama shi ne a wani gagarumin farmakin da ya biyo bayan hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi da sojoji suka yi a shekara ta 2013, wanda aka zaba bayan boren. An tsare masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya da masu kishin Islama a wani kame da aka yi masa wanda ya janyo suka a duniya.

Manyan masu fafutuka daga juyin juya hali na ci gaba da kasancewa a gidan yari, ciki har da mai fafutukar tabbatar da dimokuradiyya dan Birtaniya da Masar Alaa Abdel Fattah, wanda ya shafe fiye da shekaru goma a gidan yari. Shugaban ya yi afuwa ga manyan mutane da dama a cikin shekarar da ta gabata, amma masu sukar lamirin sun yi nuni da cewa an kama mutane da dama a halin yanzu. Tun a watan Afrilun bara, hukumomi sun saki fursunonin siyasa 1,000, amma sun tsare wasu kusan 3,000, a cewar masu sa ido kan hakkin Masar. A watan Yuli, Shugaba Sisi ya yafe wa wani mai bincike Patrick Zaki kwana guda bayan da aka yanke masa hukuncin shekaru uku, da kuma lauyan kare hakkin bil Adama Mohamed al-Baqer, wanda aka kama a shekarar 2019 a lokacin da yake halartar tambayoyin Abdel Fattah, wanda yake karewa a lokacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.