Isa ga babban shafi

Rushewar gini a Masar ya yi sanadiyar mutuwar mutane

Mutane 8 da suka hada da mutane bakwai na gida guda ne suka mutu a birnin Alkahira a jiya litinin a lokacin da wani gini a babban birnin kasar Masar ya ruguje,masu aikin ceto na ci gaba da neman mutane a cikin baragujen ginin.

Rushewar wani gini a Alexandrie na kasar Masar
Rushewar wani gini a Alexandrie na kasar Masar REUTERS/Stinger
Talla

Wata sanarwar da masu shigar da kara na bayyana cewa ginin da ke gundumar Hadayek al-Qubba da ke birnin "ya ruguje gaba daya", inda ya kashe mutane takwas.

Sanarwar ta kara da cewa, "Jami'an tsaron farin kaya sun fitar da mutane tara, da suka hada da wata mata da ta samu rauni, yayin da sauran takwas suka mutu", sanarwar ta kara da cewa "wasu biyar kuma sun samu cira da ransu tare da barin kadarorinsu  kafin faduwar ginin.

Mai gabatar da kara ya bayar da umarnin kama mai gidan, dan kwangilar da ke kula da ayyukan da kuma daya daga cikin ma’aikatansa domin amsa tambayoyi.

Kasar Masar dai ta fuskanci rushewar gine-gine da dama a cikin 'yan shekarun nan, saboda rashin kyawon yanayin wasu da kuma rashin bin ka'idojin gine-gine a hukumance,

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.