Isa ga babban shafi

Shekara 10 da sojojin Masar suka kashe masu zanga-zanga 600

Yau ne ake cika shekaru 10 cur da jami’an tsaron Masar suka kashe daruruwan mutane akasarinsu fararen hula, inda suka yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen tarwatsa gangamin masu zanga-zangar da ke goyon bayan tsohon shugaban kasar Mohamed. Morsi.

Dandalin Rabaa al-adawiya da aka kashe magoya bayan Morsi na Masar
Dandalin Rabaa al-adawiya da aka kashe magoya bayan Morsi na Masar REUTERS/Mohamed Abd El Ghany/Files
Talla

Wannan kisan kiyashin da aka yi wa magoya bayan Morsi na cikin mafi muni da aka gani a tarihin Masar, al’amarin da ya faru a dandalin Rabaa da Nahda.

Sai dai kisan ya zama musabbabin fafutukar neman sauyi hatta a kasashen Larabawa.

Har yanzu dai hukumomin Masar sun dage kan cewa, sun yi ta yin kira ga shugabannin Kungiyar ‘Yan uwa Musulmi da su kawo karshen zaman-dirshen din masu zanga-zangar , amma suka yi biris a cewarsu.

Hukumomin na Masar sun bayyana dandalin Rabaa al-Adawiya a matsayin wani sansanin yi musu tawaye a wancan lokacin, abin da ya sa suka dauki matakin magance boren.

Wadanda suka tsira daga kisan kiyashin sun shaida cewa, kwararrun jami’an harbin nesa ne suka yi ta dauke masu zanga-zangar da bindiga duk kuwa da cewa, sun yi ta daga hannayensu sama don sallamawa, amma jami’an suka ci gaba da yi musu kisan.

Koda yake hukumomin na Masar sun ce, sai da suka fara bude wa masu zanga-zangar hanyar samun tudun-mun-tsira kafin tura kwararrun maharban.

Sai dai wani rahoto na Kungiyar Human Wright Watch ya ce, akwai wasu jami’an tsaro da suka yi wa masu zanga-zangar kuri domin hana su tserewa.

Alkaluman da gwamnatin Masar ta fitar sun ce, sama da mutane 600 ne suka mutu a lokacin, amma Kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta ce, mutanen da suka mutu sun zarta dubu 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.