Isa ga babban shafi

Tsananin zafi ya tilastawa al'ummar Masar ninkaya a kogin Nilu

Sakamakon yanayin matsanancin zafin da ake fuskanta a wasu sassa na duniya ciki har da Masar da ke yankin arewacin Afrika, wasu bayanai na nuni da cewa yanzu haka al'ummar kasar sun koma zama a bakin kogin Nilu inda su ke ninkaya da nufin samun damar sanyaya jiki domin samun sa'ida. 

Wasu da tsananin zafi ya tilastawa komawa rayuwa a bakin kogi.
Wasu da tsananin zafi ya tilastawa komawa rayuwa a bakin kogi. © Laurent Cipriani / AP
Talla

Masana yanayi sun bayyana cewa yanayin tsananin zafin ya kai kololuwa a yau Alhamís yayinda ake fargabar yanayin ya ci gaba har mako mai zuwa, lamarin da ya tilastawa jama'ar kasar ta Masar tururuwa zuwa kogin na Nilu don sanyaya jikinsu.

Wani da ya ke zantawa da manema labarai a bakin kogin Khatab Ramadan ya shaida cewa bakin kogin na Nilu shi ne kadai wurin shakatawa da talakawa kan iya halarta cikin sauki amma wanda ke Askandariyya ya fi karfin su domin sai attajirai.

Wannan tsananin zafin na zuwa ne a dai dai lokacin da masana kimiyyar yanayi a Turai suka yi hasashen fuskantar tsanantar yanayin zafi a Amurka da Turai da Asia da kuma arewacin Afirka wanda ake tunanin zai tagayyara mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.