Isa ga babban shafi

Masar ta bude taron sasanta rikicin Sudan da ta ke karbar bakunci a Alqahira

Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na Masar na karbar bakoncin taron sassanta rikicin Sudan wanda ke samun halartar Firaministan Habasha Abiy Ahmed a wani ynkurin kasashen na ganin an kawo karshen zubar da jini a makwabciyar ta su.

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi lokacin da ya karbi Firaminista Abiy Ahmed na Habasha a Cairo don fara taron sasanta rikicin Sudan.
Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi lokacin da ya karbi Firaminista Abiy Ahmed na Habasha a Cairo don fara taron sasanta rikicin Sudan. © Daily News Egypt
Talla

Kasashen biyu na Masar da Habasha wadanda suka ajje rikicin da ke tsakaninsu dangane da aikin ginin madatsar ruwan da Abiy Ahmed ke yi akan kogin Nilu, yayin tattaunawarsu a fadar gwamnatin Masar sun sha alwashin aiki tare don magance rikicin na Sudan.

Sanarwar faro taron na yau da kakakin shugaba Sisi ke fitarwa tun a jiya laraba na zuwa ne a dai dai lokacin da Sudan ta yi watsi da yunkurin kungiyar kasashen gabashin Afrika na girke dakarun wanzar da zaman lafiya a Khartoum don yayyafawa yakin kasar ruwa, bayan da bangaren gwamnatin Sojin kasar ya zargi Kenya da goyon bayan dakarun RSF.

Taron Wanda ke matsayin mafi girma tsakanin kasashen yankin da Masar ta kira don sasanta rikicin na Sudan ya samu halarta shugabannin kasashen makwabta ko da ya ke sanarwar bata bayyana sunayen shugabannin ko kuma kasashen da suka aike da wakilci ba.

Taron na Cairo a yau alhamis na zuwa ne bayan mabanbantan yunkurin Diflomasiyya daga kasashen da ke makwabtaka da Sudan don kawo karshen rikicin kasar na kusan watanni 4, baya ga kokartawar da kasashen Amurka da Saudi Arabia suka a lokuta da dama wanda ya kai ga tsagaita wuta a lokuta daban daban.

Zuwa yanzu yakin na Sudan da aka faro ranar 15 ga watan Aprilu bayan baraka tsakanin jagoran mulkin Sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da kuma Mohamed Hamdan Daglo da ke jagorantar dakarun RSF, akalla fararen hula dubu 3 suka rasa rayukansu yayinda wasu miliyan 3 suka tsere daga matsugunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.