Isa ga babban shafi
Nijar

Yara 12 sun mutu a Nijar sakamakon harin Dorina

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar yara ‘yan makaranta 11 da kuma wani mutum daya, a hatsarin da wani karamin kwale-kwale ya yi sakamakon harin da wata dorina ta kai ma sa, a kauyen Libore da ke kusa da birnin Yamai.

Kauyen Libore a Jamhuriyyar Nijar inda Dorita ta kai wa Dalibai hari
Kauyen Libore a Jamhuriyyar Nijar inda Dorita ta kai wa Dalibai hari pencilsforkids
Talla

Al’amarin ya faru ne a ranar Litinin, kuma an bayyana yaran da suka mutu ‘yan tsakanin shekaru 12 zuwa 13.

Ministar kula da makarantun Sakandare Aichatou Oumani, tace dalibai 12 ne a cikin kwale kwalen da suka hada da dalibai mata bakwai da maza biyar.

Alhaji Mustafa Kadi, Shugaban wata kungiyar kare hakkin bil’adama, ya bukaci gwamnati da ta dauki matakai domin hana sake faruwan hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.