Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

An kulla yarjejeniyar Zaman lafiya tsakanin Kiir da Machar

Bangaren gwamnati da na ‘yan tawayen Sudan ta Kudu sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya inda suka sake alkawarin kawo karshen watanni takwas da aka kwashe ana tashin hankali a kasar.

Riek Machar da Salva Kiir a birnin Addis Abeba..
Riek Machar da Salva Kiir a birnin Addis Abeba.. REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Bayan sanya hannu akan sabuwar yarjejeniyar ta zaman lafiya, shugabanin kasashen dake yankin Gabashin Afrika da ake kira IGAD, sun bukaci bangarorin biyu da suka kafa gwamnatin hadin-kai a cikin kwanaki 45 masu zuwa.

Fira Minsitan Habasha Haillemariam Desalegn ya ce a matsayinsu na Yanki, duk wanda ya karya yarjejeniyar da aka sanyawa hannu zai fuskanci hukunci.

Desalegn ya ce suna aikewa da sako karara ga shugaba Salva Kiir da korarren mataimakinsa Riek Machar. cewar ba za a lamunce da samun duk wani tsaiko ba wajen aiwatar da yarjejeniyar, lura da yadda ake ci gaba da rasa rayuka a cikin kasar.

A baya dai bangarorin biyu sun sanya hannu akan irin wannan yarjejeniya har sau uku amma babu wadda tayi tasiri.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.