Kiir da Machar zasu hau teburin sulhu
Ma’aikatar harakokin wajen Sudan ta Kudu tace Shugaban kasar Salva kiir ya kama hanya zuwa Addis Ababa domin halartar zaman teburin sulhu tare da Tsohon Mataimakinsa kuma kwamandan ‘Yan tawaye Riek Machar da suke rikici da juna tun a watan Disemban bara.
Wallafawa ranar:
Kasashen duniya suna fatar samu jituwa a tattaunawar tsakanin Machar da Kiir domin kawo karshe rikicin kasar da janyo hasarar rayuka da dama.
Tun a daren Alhamis ne, rahotanni suka ce Riek Machar ya isa birnin Addis Ababa inda za’a yi zaman tattaunawar ta keke da keke tsakanin shi da shugaba Salva Kiir da kuma mai shiga tsakani shugaban kasar Habasha.
Dr Laraba Abdullahi
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu