Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Machar zai halarci zaman sulhu da Kiir

Shugaban 'Yan tawayen Sudan ta Kudu Reik Machar ya yi alkawalin zai halarci zaman sulhu a Addis Ababa, da za'a gudanar a ranar Juma'a tare da Shugaba Salva kiir, kamar yadda Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya tabbatar bayan ya kai ziyara a kasar da ke fama da rikici.

Shugaban 'Yan tawayen Sudan ta kudu Riek Machar
Shugaban 'Yan tawayen Sudan ta kudu Riek Machar REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Ban ki-Moon yace Shugaban kasar Salva Kiir ya tabbatar masa da muradinsa na zama teburin sulhu da Riek Machar tsohon mataimakinsa da suke yaki da juna, kamar yadda Machar ya tabbatar wa gwamnatin Habasha akan zai halarci zaman tattaunawar.

Rikicin sudan ta kudu dai yanzu ya kazance ne tsakanin dakarun da ke biyayya ga bangaorirn biyu, inda suke yakar juna domin karbe ikon yankunan da ke da arzikin fetir da kasar ke yin dogaro bayan ta balle daga Sudan.

Tun kafin ziyarar Ban ki-moon a kasar, Ofishin Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa akalla mutanen kasar Miliyan daya zasu fuskanci yunwa saboda rikicin da ake gwabzawa tsakanin dakarun gwamnatin Salva Kiir da Reik Machar wadanda kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka zarga da aikata laifukan yaki.

A ranar Juma'a mai zuwa ake sa ran za'a gudanar da tattaunawar ta sulhu tsakanin Salva Kiir da Machar domin kawo karshen rikicin, kodayake akwai alamun za'a dage tattaunawar domin ba Machar damar halarta zaman sulhun daga inda ya ke jagorantar 'Yan tawaye.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.