Isa ga babban shafi
Mali

Mali: Sanogo ya shiga yajin cin abinci

Jagoran Juyin Mulki a kasar Mali Kaftin Amadou Sanogo ya shiga yajin cin abinci domin nuna adawa da canza masa kurkuku da aka yi daga Bamako zuwa Selingue da ke kudancin kasar, kamar yadda lauyansa Toure Harouna ya tabbatar.

Janar  Amadou Sanogo wanda ya jagoranci hambarar da gwamnatin Amadou Toumani Toure na Mali
Janar Amadou Sanogo wanda ya jagoranci hambarar da gwamnatin Amadou Toumani Toure na Mali REUTERS/Joe Penney
Talla

An cafke Janar Sanago ne bayan tuhumarsa da sace wasu Sojoji tare kashe su wadanda suka taimaka ya kifar da gwamnatin Amadou Toumani Toure.

Akwai gawawwakin mutane kusan 30 da aka gani a cikin wani makeken Kabari a cikin barikin Sojoji da ke Kati.

Wata majiyar Soji a Mali ta tabbatar wa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa Janar din na Soja ya shiga yajin cin abinci.

A watan Nuwamban bara ne aka cafke Sanogo tare da wasu makusantansa 32 amma an taba sakinsu daga gidan yarin a watan Janairu bayan sun shiga yajin cin abinci a watan Janairu domin adawa da halin yadda suke rayuwa a gidan yari.

Juyin mulkin da Janar Sanogo ya jagoranta, shi ya haifar da rikici a Mali inda Mayakan Jihadi a kasar suka samu damar karbe ikon yankin arewaci kafin Faransa ta taimaka a kwato yankin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.