Isa ga babban shafi
Burundi

Sabuwar doka game da aikin jarida a kasar Burundi

Majalisar Dattawan kasar Burundi ta amince da wani daftarin doka wanda kungiyoyin ‘yan jarida na kasar ke kallo a matsayin mai tauye hakkokin da ma’aikatan yada labarai ke da su a kasar.

Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza.
Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza. AFP/Pierre Andrieu
Talla

Kafin Majalisar Dattawan ta amince da wannan daftari, tuni takwararta Majalisar Dokoki ta amince da shi. Kuma duk da ‘yan sauye-sauyen da Majalisar dattawan ta aiwatar kafin amincewa da daftarin, bayanai sun yi nuni da cewa har yanzu akwai wasu bangarori na dokar wadanda ake kallo a matsayin kangi ga kafafen yada labarai da kuma ‘yan jaridu na kasar matukar dai aka soma aiki da ita.
Alexandre Niyungeko, shugaban kungiyar ‘yan jaridu a kasar ta Burundi, ya bayyana sabuwar dokar a matsayin wani koma-baya ga dimokuradiyyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.