Isa ga babban shafi
Somaliya

Kungiyar Al shabab ta kashe mayakanta uku saboda cin amana

Kungiyar Al shabab ta Somalia tace ta kashe wasu Mambobinta guda uku saboda cin amanar kungiyar wajen taimakawa dakarun Amurka kashe wasu ‘Yayanta. Wannan ne kuma karo na farko da kungiyar ta kashe mayakanta saboda cin amana.

Wasu Mayakan kungiyar al Shabab a Somalia
Wasu Mayakan kungiyar al Shabab a Somalia
Talla

A watan Janairun bara, kungiyar al Shabab tace wani harin Bom ya kashe Bilal el Berjawi dan asalin kasar Lebenon da ke dauke da Fasfo na Birtaniya.

Kungiyar tace ta kashe mambobinta guda biyu wadanda suka taimaka aka kashe Sheikh Mohamed Abu Abdallah, Gwamnan lardin Shabelle tare da wani mamba da aka tabbatar dan leken asirin kasar Birtaniya ne.

Kungiyar ta shaidawa kamfanin dillacin Labaran Reuters cewa tana ci gaba da gudanar da bincike domin zakulo wasu daga cikin munafukan ‘yayanta.

Gwamnatin Somalia tace akwai dinbim mayaka da suka shiga kungiyar daga kasashen Afghanistan da Pakistan wasun su daga Amurka da Birtaniya domin karya kungiyar.

A bara ne aka fatattaki kungiyar Al shabab daga birnin Mogadishu, kuma yanzu haka kungiyar tana fuskantar matsin lamba daga dakarun Kenya da Habasha da kuma dakarun kungiyar kasashen Afrika domin kare yaduwar kungiyar daga Somalia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.