Isa ga babban shafi
Somalia

Shugabannin Wasanni biyu sun mutu a Somalia

A kasar Somalia kuma shugaban hukumar kwallon kafar kasar da shugaban kwamitin wasannin Olymoics dukkaninsu sun mutu sakamakon wani harin bom na kunar bakin da ya tashi da wata mata a Mogadishu.

Gawar Shugaban hukumar kwallon kafar kasar Somalia kwance a kujera inda wani bom ya tashi a kunar bakin wake a Mogadishu.
Gawar Shugaban hukumar kwallon kafar kasar Somalia kwance a kujera inda wani bom ya tashi a kunar bakin wake a Mogadishu. REUTERS/Omar Faruk
Talla

Shugaban kwmaitin wasannin Olympic Aden Yabarow da shugaban kwallon kafar Somali, Said Mohamed Nur suna cikin mutane 10 da suka gamu da ajalinsu a wani bukin da suka halarta a Mogadishu

Al’amarin dai ya faru ne a lokacin da Fira Ministan kasar Abdiweli Mohamed Ali zai gabatar da jawabi. Sai dai kakakin gwamnatin kasar yace Fira Ministan bai samu rauni ba inda ake tunanin an kitsa harin kunar bakin waken ne domin kashe Fira Ministan na Somalia

Tuni dai shugaban hukumar kwallon kafa ta Dunya Sepp Blatter ya mika sakon ta’aziyar shi tare bayyanna kokarin hukumar wajen kyautata rayuwar al’ummar Somalia ta hanyar wasanni.

Shugaban hukumar kwallon kafar Nahiyar Afrika Issa Hayatou, ya mika sakon ta’zaiyar shi inda yace wannan wata ranar bakin ciki ce ta biyu a Afrika bayan samun mutuwar mutane 70 a filin wasan Pord Said na kasar Masar.

Wannan harin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kwamitin wasannin Olymoic na Somalia ke shirye shirye zuwa birnin Landon a wasannin Olympics da za’a fara a watan Yuli.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.