Isa ga babban shafi
Somaliya

Yan Fashin ruwan Somaliya sun nemi sakin 'yan uwansu

'Yan Fashin jiragen ruwan Somaliya, dake rike da jirgin ruwan Panama da suka kama a watan da ya gabata, sun bukaci sakin 'yan uwansu da aka kama, domin suma su saki jirgin.Daya daga cikin mutanen dake rike da jirgin, Yusuf Ali, ya ce zasu karbi dan karamar diyya, da kuma sakin 'yan uwansu kafin su saki jirgin mai dauke da kaya zuwa yankin Somaliland. 

Talla

Yanzu haka kasashen duniya sun suna taimakawa domin wanzar da zaman lafiya a kasar ta Somaliya data kwashe shekaru 20 cikin tashin hankali. Babban jami'an MDD dake kasar Augustine Mahiga, ya zargi 'yan majalisun kasar da haifar da tsaiko, wajen kankame hanyoyin tabbatar da zaman lafiya.

Gwamnatin rikon kwaryar kasar tana smaun tallafin kasashen duniya. Inda yanzu haka aka mayar da sufurin jiragen sama. Kuma harkokin rayuwa suka fara daidaita musamman a Mogadishu babban birnin kasar ta Somaliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.