Obama ya tabbatar da sabanin da ke tsakaninsa da Netanyahu
Shugaban kasar Amurka, Barrack Obama, ya fito fili karara inda ya bayyana cewa akwai sabani tsakaninsa da firaminsitan Isra’ila Benyamin Netanyahu
Wallafawa ranar:
Obama ya bayyana haka ne, sakamakon yadda Netanyahu ke haddasa tarnaki dangane da shirin samar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Palasdinu.
A lokacin zantawa da manema labarai, Obama ya kara da cewa, a lokacin da Netanyahu ke gudanar da yakin neman zabensa, ya tabbatar da kudirinsa na cewa, ba bu batun kafa kasar Palasdinu, matukar yana kan karagar mulki.
To sai dai shugan Amurkan, ya tabbatar cewa Kasarsa za ta ci gaba da huldar diplomasiyya da Isra’ila, amma ba za ta amfani Benjamin Netanyahu ba, nan da shekaru 7 masu zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu