Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka zata yi nazarin dangantakarta da Isra'ila

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana cewa, kasarsa zata sake nazarin dangantakarta da Isra’ila, bayan da Firaminista Benjamin Netanyahu ya lashe babban zaben kasar  

Shugaban Amurka, Barack Obama.
Shugaban Amurka, Barack Obama.
Talla

Mr Obama yace hukumomin birnin Washigton zasu sake nazari, kan kariyar da suke baiwa kasar ta Yahudu, a zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Kwanaki 2 bayan fidda sakamakon zaben da ya bada mamaki, sannan fadar gwamnatin Amurka ta White House tace, shugaba Obama ya taya Netanyahu murnan lashe zaben, a wata zantawa dashi ta wayar salula, duk da cewa, tattaunawar, ba ta yi armashi ba.

A bangare guda, Ma’aikatar tsaron Isra’ila, ta bayyana cewa, huldar samar da tsaro tsakanin kasashen biyu, zata daure, duk da takun sakan dake tsakin Obama da Netanyahu.

A lokacin gudanar da yakin neman zabensa, Netanyahu ya lashi takobin cewa, idan ya lashe zabe, to zai rusa batun samar da ‘yantacciyar kasar Palasdinu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.