Isa ga babban shafi
Rasha-Syria-Amurka

Rasha zata karbi bakuncin taron kawo karshen rikicin kasar Syria

Yau shugabannin ‘yan tawayen kasar Syria da wakilan gwamnatin shugaba Bashar Bashar al-Assad suka fara tattaunawa, don neman mafita a rikicin kasar. Sai dai akwai alamun zai yi wuya taron na kasar Rasha ya kawo karshen tashin hankalin kasar, da yayi sanadiyyar rasa ran dubun dubatar ‘yan kasar ta Syria.Taron, da za ayi tsakanin kungiyoyin dake adawa da hukumomin birnin Damascus, da gwamnatin kasar ta Syria, zai gudana ne karkashin jagorancin jakadan kasar ta Syria a Majalisar Dinkin Duniya Bashar Jaafari.Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gumurzu tsakanin mayakan Kurdawa da ‘yan kungiyar ISIS, a kusa da garin Kobane, dake kan iyakar kasar da Turkiya.Karfin da kungiya ta ISIS ke kara samu ya canza yadda kasashen yammacin duniya ke fuskantar rikicin na Syria, lamarin da ake gani zai sa bangarorin dake rikici da juna zasu nemi hade kai, da nufin murkushe abokin gaba guda.Sai dai manayan masu adawa da shugaba Assad sun kaucewa taron, inda suke zargin Rasha, wadda aminiyar shugaban ce, ba zata yi adalci ba. 

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad REUTERS/SANA/Handout via Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.