Isa ga babban shafi
Iraqi-syria

An kwato yankin husaybah daga hannu ISIL

A wani harin da suka kaddamar a safiyar yau Assabar Dakarun kasar Iraqi da sojojin sa kai na 'yan shi'a sunyi nasara kwato yankin Husaybah da ke gabashin birinin Ramadi daga hannu ‘yan tawayen ISIL mai nisan kilomita 7 daga birnin. karon farko tun bayan faduwar lardin Anbar a hannu 'yan tawayen.

Sojoji a Ramadi
Sojoji a Ramadi REUTERS/Stringer TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

A dai cikin kwanakin baya ne, mayakan na ISIL suka sanar da kwace ikon Ramadi, da ke da muhimmaci a gabas ta tsakiya kana daga baya suka kara kwace Palmyra mai dimbin tarihi

Sai dai dakarun sojin na iraqi da ke tunkara ISIL din sunce sun fara samun nasara akan Mayakan

Mukaddashin Jami'in hukumar taimakon agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Dominik Bartsch ya baiyana damuwar sa akan halin da mutanen da suka tsere daga Ramadi suke ciki a gabar wata gada da ke hanyar shiga Bagadaza musamman mata da yara kanana da kuma tsofafi.

Jami'ai sun ce sojoji da mayakan sa kai na shi'a sun fatattaki 'yan tawayen daga garin Hussaiba dake gabashin Ramadi a wani luguden wuta da sukayi akan mayaka masu da'awar kafa kasar musulunci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.