'Yan tawayen Yemen na kokarin shiga Mafakar Shugaban Kasar
Akalla Mutane 30 sun mutu a wata musayar wuta tsakanin Dakarun Gwamnatin Kasar Yemen da ‘Yan tawayen da ke kokarin kutsa kai domin shiga birnin Aden, inda Shugaban Kasar Abdul-Rabuh Mansur Hadi ke da mafaka
Wallafawa ranar:
A bangare guda, bayan karbe ikon filin jirgin sama dake birnin Taez da sansanin soji mai nisan kilimiter 180 da ke arewacin birnin Aden, ‘Yan tawayen sunyi ajalin wasu mutane 5 wadanda ke zanga-zangar adawa da ayyukansu
Mayakan sun yi nasarar karbe ikon wurare da dama a kasar Yemen, amma a yanzu birnin Aden suke fako, inda shugaba Hadi ya tsere bayan daurin talala da ga hannun mayakan.
Masana dai na ganin cewa, idan har mayakan suka yi nasarar karbe ikon Aden, to hakika kasar zata fada cikin rikicin da zai zama matsala ga sauran kasashen duniya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu