Isa ga babban shafi
Najeriya

Ban Ki-moon ya yaba wa Zaben Najeriya

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya taya Najeriya murnar samun nasarar gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘Yan Majalisu cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da an samu wani tashin hankali ba.

Zaben Najeriya na 2015.
Zaben Najeriya na 2015. REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

A cikin wata sanarwa daga birnin New York, Ban Ki-moon ya bukaci ‘Yan Najeriya su ci gaba da bin hanyoyin kaucewa rikici domin tabbatar da zaman lafiya har a bayyana sakamakon zaben kasar.

Ban ya la’anci hare hare da Mayakan Boko Haram suka kai a wasu yankunan arewa maso arewacin Najeriya domin dagula lamurran zabe a kasar.

Tawagar kungiyar Tarayyar Turai da ke sa ido a zaben sun yi kira ga shugabannin siyasa su kauracewa duk wani abu da zai haifar da rikici a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.