Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojoji na fada da Boko Haram a kusa da Bauchi

Rahotanni daga Najeriya na cewa dakarun kasar suna can suna gwabza fada da mayakan Boko Haram a kusa da garin Bauchi, rikicin na zuwa ne kuma a yayin da wasu yankunan kasar ke gudanar da zaben shugaban kasa a rana ta biyu.

Sojan Najeriya, da ke fada da Boko Haram
Sojan Najeriya, da ke fada da Boko Haram RFI/OR
Talla

Wata majiyar tsaro tace Sojoji sun tunkari Mayakan Boko haram a kauyen Dungulbe bayan sun doshi garin Bauchi.

Majiyar tace Sojojin sun kai wa Mayakan hare hare ta kasa da kuma jiragen sama.

Wani mazauni kauyen Dungulbe ya ce mayakan sun iso kauyen ne cikin motoci kimanin 20 da safe, tare da kafa sansani domin shirin kaddamar da hare hare.

Rahotanni sun ce mayakan sun ratso ne ta garin Alkaleri, inda suka kai hare hare a gine ginen gwamnati da shingen masu bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.