Isa ga babban shafi

'Yar Africa ta Kudu ta lashe gasar sarauniyar kyau ta duniya

Rolene Strauss ‘yar kasar Africa ta kudu itace ta lashe gasar sarauniyar kyau ta duniya da aka gudanar a birnin London na kasar Brittaniya, na wannan shekarar ta 2014. Rolene Strauss mai shekaru 22 dai ta lashe gasar daga cikin mata 121 da suka tsaya takarar fidda gwanar kyau ta duniya, gasar da mutane akalla biliyan daya suka kalla ta kaffofin talabijin a sassan duniya daban daban. Bayan sanar da ita a matsayin wacce ta lashe gasar, Strauss cike da mamaki ta bayyana farin cikin ta, inda ta sadaukar da kanbun nata ga al’ummar kasar ta, wato Africa ta kudu.Sarauniya daga kasar Hungary Edina Kulscar ita tazo ta biyu yayin da Elizabeth Safrit daga kasar Amurka tazo ta uku. A cikin nauyin da suka rataya a wuyan sabuwar sarauniya sun hada da kai ziyarar aiki kasar Honduras domin karrama sarauniyar kyau ta kasar da wani wanda ba’a san kowanene ba ya hallaka a watan da ya gabata.Gasar sarauniya kyau a duniya dai ana gudanar da ita ne sau daya a kowacce shekara domin fidda macen da tafi kowacce kyau a duniya.  

Sarauniyar kyau ta shekarar 2014, 'yar kasar Africa ta kudu Rolene Strauss
Sarauniyar kyau ta shekarar 2014, 'yar kasar Africa ta kudu Rolene Strauss
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.