Isa ga babban shafi

Ana cecekuce kan jiragen ruwan yaki da Tompolo ya sayo a Nigeria

A karshen makon daya gabata wasu rahotanni suka nuna cewa tsohon dan bindiga na yankin Neja Delta a Nigeria, Chief Government Ekpemupolo da aka fi sani da Tompolo, ya shiga da wasu wasu jiragen ruwan yaki 7 zuwa kasar. Wannan ya jefa fargaba a zukatan ‘yan kasar, musamman ma mazauna yankin na Neja Delta mai arzikin man fetur, da aka dade ana fama da rikice rikice.Rahotanni na cewa an sayo jiragen ruwan ne daga kasar Norway, ta hannun wani kamfani mai zaman kanshi a madadin kamfanin Global West Vessel Services, mallakin Tompolo.Tompolo na daya daga cikin tsagerun yankin Neja Delta da suka amince su ajiye makamai, sakamakon afuwar da hukumomin Nigeria suka yi musu a shekarar 2009.A halin yanzu dai kamfanin na Tompolo nada kwangilar miliyoyion Nairori da gwamnatin taraiyyar Nigeria ta bashi, don kula da ruwayen Nigeria, da nufin hana satar mai.Masani kan Harkokin Tsaro Husaini Munguna yace ba wani mutum ko kamfanin dake da damar sayo jiragen yaki ba tare da hannun gwamnati ba, sai dai hukumomin tsaron kasar su sayo da kansu.Malam Husaini Munguno ya nemi a gudanar da bincike kan zargin.Har yanzu hukumomin tsaron, da na NIMASA dake kula da tsaro a ruwayen Nigeria, basu ce komai ba kan lamarin. 

Wasu jiragen ruwan yaki
Wasu jiragen ruwan yaki DR net
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.