Isa ga babban shafi

PSG ta fitar da Barcelona daga gasar zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta fitar da Barcelona daga gasar Zakarun Turai, bayan lallasa ta a gida da ci 4 da 1 yayin wasan kwata final a daren ranar Talata.

Mai horas da kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona
Mai horas da kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona REUTERS - Sarah Meyssonnier
Talla

A wasan farko dai Barcelona ce ta je gidan PSG inda ta yi nasarar zura mata kwallo 3 yayin da ita kuma PSG ta ci 2, inda jimillar kwallayen na wasanni biyu da suka buga gida da waje 6 da 4 kenan.

Dama gabanin wasansu na zagayen kwata final din na daren Talata ɗan wasan PSG Kylian Mbappe, ya aika sakon gargadi ga kungiyar Barcelona.

'Yan wasan PSG na murnar chasa Barcelona a Kwat Fainal
'Yan wasan PSG na murnar chasa Barcelona a Kwat Fainal REUTERS - Juan Medina

Tarihi ya nuna Mbappe ya taɓa cin Barcelona ƙwallaye uku a wasa guda a gasar ta Zakarun Turai, a shekarar 2021 inda PSG ta doke Barcelona da ci 4 da 1 a haduwar farko ta wasansu da aka buga a birnin Paris.

A wasan na jiya ma tarihi ya kusa maimaita kansa inda Mbappe ya zura ƙwallaye biyu rigis a ragar Barcelona.

Klyan Mbappe yana murna bayan cin kwallo
Klyan Mbappe yana murna bayan cin kwallo REUTERS - Juan Medina

A wani wasan na kwata final ɗin da aka fafata a daren na ranar Talata, ƙungiyar Atletico Madrid ta yi adabo da gasar ta bana bayan da Borussia Dortmund ta lallasa ta da ƙwallaye 4 da 2.

A baya dai Atletico Marid ta caskala Dortmund da ci 2 da 1 a wasan farko da suka buga.

Yanzu haka Dortmund za ta fafata wasa da PSG a wasan kusa da na karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.