Isa ga babban shafi

Leverkusen ta lashe gasar Bundesliga ta farko cikin shekaru 120

A karon farko cikin shekaru 120 bayan kafuwar kungiyar kwallon kafa ta Bayer Leverkusen ta lashe gasar Bundesliga ta kasar Jamus tun kafin a kai ga karkareta.

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta bayern Leverkusen
Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta bayern Leverkusen REUTERS - Wolfgang Rattay
Talla

Nasarar ta Leverkusen na zuwa ne bayan da ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Werder Bremen da ci 5 da nema a daren ranar Lahadi.

Kungiyar ta Leverkusen karkashin mai horas wa Xavi Alonso ta kawo karshen tarihin kungiyar Bayern Munchen da ta shafe shekaru 11 tana jan zarenta a gasar.

Kazalika Bayern Leverkusen ta kafa wani tarihin a kakar wasannin shekarar nan, inda ta buga wasanni 43 rigis a gasannin daban-daban ba tare da yin rashin nasara ba.

A yanzu haka dai Leverkusen za ta mayar da hankali ne kan gasar Europa inda take neman kai wa mataki na kusa da na karshe bayan ta doke Westam Ham ta Ingila da ci biyu da nema a makon da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.