Isa ga babban shafi

Liverpool ta sha duka a hannun Atalanta har gida da kwallaye 3 da nema

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sha duka a hannun Atalanta cikin daren jiya Alhamis, da kwallaye 3 da nema karkashin gasar Europa, wato gasa ta biyu mafi daraja a Turai, wasan da masana ke ganin shi ne mafi muni ko kuma mafi kunya da Reds ta fuskanta karkashin jagorancin Jurgen Klopp.

Mohamed Salah na Liverpool.
Mohamed Salah na Liverpool. © Reuters/Jason Cairnduff
Talla

Har gida ne Atalantar wadda ta yi tattaki daga Italiya zuwa Anfield ta lallasa Liverpool, yanayin da ba safai aka saba gani ba, musamman karkashin jagorancin Klopp na shekaru 8.

Wasan na jiya zai iya kasancewa na karshe da Klopp zai karbi bakoncin wata kungiyar a Anfield karkashin manyan gasar Turai da suka kunshi Europa da ya sha kaye ko kuma yayarta ta zakarun Turai, lura da yadda ya ke shirin ajje aiki a kashen wannan kaka.

Kafin shan kayen na jiya, shan kaye na farko mafi muni da Liverpool ta gani har Anfield karkashin jagorancin Klopp shi ne lokacin da Real Madrid ta ratata mata kwallaye 5 da 2 a watan Fabarairun 2023 karkashin gasar zakarun Turai wanda ya kawo karshen wasanni 33 da tawagar ta yi ba tare da an doketa a gida ba.

Iya nasara kan Liverpool a gidanta wato Anfield karkashin kowacce gasa dai ba abu ne mai sauki ba.

A karshen wannan Kaka ne manajan Bajamushe ya ke shirin barin kungiyar sai dai ya yi fatan kai Liverpool wasan karshe na Europa kamar yadda ya kai ta wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai har sau 3 tare da lashe kofin sau 1.

Yayin wasan na jiya dai ‘yan wasan na Klopp sun rika tafka kura-kura wanda ya bai wa Atalanta da ke matsayin ta 6 a teburin Seria A damar ratata kwallayen har 3 ba tare da sun iya farke ko guda daya ba.

Atalanta ta kafa tarihin zama kungiya ta biyu da ta shiga Anfield ta zura kwallaye ba tare da an farke ba karkashin gasar Turai bayan Barcelona a 2007.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.