Isa ga babban shafi
GASAR TURAI

Ana ci gaba da tafka mahawara a kan dalilin hana Arsenal fenariti

Turai – Masana harkar kwallon kafa na ci gaba da tafka mahawara a kan yadda alkalin wasa Glenn Nyberg hana kungiyar Arsenal damar buga fenariti gab da kammala karawar da kungiyar ta yi da Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Bukayo Saka
Bukayo Saka © Kin Cheung/AP
Talla

'Dan wasan gaba na Arsenal, Bukayo Saka cikin gudu ya yanka mai tsaron gida Manuel Nuer, amma sai ya ki janye kafar sa abinda ya kai ga Saka ya yi karo da ita, ya kuma fadi nan take.

Amma sai alkalin wasan ya shafawa idan sa bula ya kuma hana Arsenal daman buga fenaritin da ake ganin ka iya sauya sakamakon wasan da aka tashi da ci 2-2.

Cikin fushi Saka ya bi alkalin lokacin da ya busa tashi domin jin dalilin da ya sa ya hana ki basu fenariti, amma bai amsa masa ba.

Mutane da dama na kallon abinda ya faru a matsayin fenaritin da ke iya taimakawa Arsenal a wasan, amma kuma hakan bai yiwu ba.

Tsohon kaftin din Manchester United Rio Ferdinand da takwaran sa na Arsenal Martin Keown sun ce basu ga dalilin da ya sa alkalin wasa ya hana kungiyar Arsenal damar da suka samu ba.

Ferdinand da Keown dake gabatar da shari lokacin karawar, sun ce da alkalin wasan ya nemi taimakon na'uarar dake tantance abinda ya faru da ake kira VAR watakila da ya gano kuskuren da ya yi wajen hana Arsenal bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Daga bisani alkalin wasan Nyberg ya bayyana dalilin kin bai wa Arsenal wannan bugu a matsayin karamin laifin da bai gamsar da shi ba a matakin kwata final.

Sakamakon karawar ya nuna cewar sai a makon gobe za'a tantance kungiyar dake iya zuwa matakin kusa da na karshe a karawar da kungiyoyin biyu za su sake yi a Munich.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.