Isa ga babban shafi
Europa

Celtic ta rike Inter a Glasgow

Wasa tsakanin Inter Milan da Celtic an tashi ne ci 3 da 3, wasan da kungiyoyin biyu suka maimaita tarihi a wasan karshe da suka fafata a shekarar 1967. Nan gaba sai Celtic ta yi da gaske a fafatawa ta biyu a San siro saboda yawan kwallayen da Inter ta zira a ragarta a Glasgow.

'Yan wasan Kungiyar Celtic ta Scotland
'Yan wasan Kungiyar Celtic ta Scotland celticfc
Talla

Everton ta Ingila ta doke Young Boys ta Switzerland ne ci 4 da 1, kuma Rumelu Lukaku ne ya yi ruwan kwallaye uku a raga.

Liverpool ta samu sa’ar Besiktas ne ci 1 da 0 a Anfield, yayin da Tottenham ta yi kunnen doki da Fiorentina a White Hart Lane.

Bayan kammala wasan Liverpool jagoran kungiyar Steven Gerrard ya soki Mario Balotelli akan yadda ya yi kaka-gida ya karbe bugun fanariti a hannun Jordan Henderson.

Henderson ya yi shirin harba fanariti amma Baletolli ya karbe, lamarin da Gerrard ya bayyana rashin jin dadinsa wanda ke bayan fagen wasan saboda rauni.

Wolfsburg ta Jamus ta doke Sporting Lisbon 2 da 0.

Kungiyoyin da suka smau nasara a jiya Alhamis a Europa league sun hada da Napoli da Sevilla da Zenit St Petersburg da Guingamp da Villarreal da kuma Ajax.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.