Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Zakarun Turai: Celtic ta sha kashi

Legia Warsaw ta haramta wa Kungiyar Celtic ta Scotland shiga gasar zakarun Turai sau uku a jere bayan ta lallasata da jimillar kwallaye ci 6 da 1 a fafatawar neman samun hurumin shiga gasar a bana. Yanzu Celtic zata gwada sa’a ne domin samun shiga gasar Europa league, bayan sau uku a jere ana fafatawa da ita a rukunin farko na gasar zakarun Turai.

'Yan wasan Kungiyar Celtic ta Scotland
'Yan wasan Kungiyar Celtic ta Scotland celticfc
Talla

Haka kuma Zenit St Petersburg ta Rasha ta tsallake zuwa buga wasannin share fagen shiga gasar zakarun Turai da jimillar kwallaye uku a ragar Limassol ta Cyprus.

Malmo ta Switzerland ta tsallake ne da yawan kwallayen da ta jefa a gidan Sparta Prague ta Jamhuriyyar Czech inda suka tashi da jimillar kwallaye ci 4 da 4 a tsakaninsu.

A gobe Juma’a ne za’a hada kungiyoyin da zasu kara da juna domin cike gibin rukunin farko na gasar zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.