Isa ga babban shafi
La liga

Clasico: Suarez ya dawo

Kocin Barcelona Luis Enrique ya tabbatar da cewa Luiz Suarez zai fara taka leda a karawar Clasico da sabuwar kungiyar shi Barcelona da za ta yi karawar kece raini da Real Madrid a ranar Assabar a filin Santiago Bernabeu.

'Yan wasan Barcelona Neymar da Luis Suarez
'Yan wasan Barcelona Neymar da Luis Suarez Reuters
Talla

Real Madrid da Barcelona zasu yi haduwar Clasico ne karo na 229, yayin da gwanin Cizo Luis Suarez zai yi haskawa ta farko bayan kammala zaman hukuncin haramcin wasanni na tsawon watanni hudu saboda cizon Giorgio Chiellini na Italiya a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Luis Suárez, na  FC Barcelona,
Luis Suárez, na FC Barcelona, REUTERS/Gustau Nacarino

Wasan zai ja hankali ne saboda dawowar Suarez da Barcelona ta saya kudi euro Miliyan 9 da kuma adawar da ke tsakanin manyan kungiyoyin biyu a Spain.

Zuwa yanzu Barcelona ce saman teburin La liga da maki 4 tsakaninta da Real Madrid da ke matsayi na uku bayan Sevilla a matsayi na biyu.

Wani batu da zai mamaye kanun labaru idan an kammala wasan shi ne idan Messi ya zira kwallo a raga a wasan da za’a gudanar a karshe mako, domin zama limamin raga a tarihin La liga.

Tazarar kwallo guda kacal ne ya raba Messi da Talmo Zarra tsohon dan wasan Athletic Bilbao mai yawan kwallaye 251 a raga.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.