Isa ga babban shafi
Brazil 2014

Italiya ta doke Ingila

Mario Balotelli ya taimakawa kasar Italiya doke Ingila ci 2 da 1 a gasar cin kofin duniya da manyan kasashen biyu daga Nahiyar Turai suka fafata a zagayen farko. Kasar Costa Rica kuma ta doke Uraguay ci 3 da 1.

Dan wasan Italiya Mario Balotelli ya jefa kwallo a ragar Ingila
Dan wasan Italiya Mario Balotelli ya jefa kwallo a ragar Ingila REUTERS/Francois Marit
Talla

Ana minti 50 ne bayan dawo daga hutun rabin lokaci Balotelli ya jefa wa Italiya kwallo ta biyu a ragar Ingila ana kunnen doki.

Claudio Marchisio ne ya fara zira wa Italiya kwallo a raga ana minti 35 da fara wasa, yayin da kuma Daniel Sturridge ya farke wa Ingila kwallon.

Yanzu haka dai Italiya da Costa Rica ke jagorancin rukuninsu na D, bayan Costa Rica ta lallasa Uraguay ci 3-1.

A ranar Alhamis ne Ingila zata hadu da Uraguay inda dukkanin kasashen zasu nemi samun nasara don samun tsallakewa zuwa zagaye na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.