Isa ga babban shafi
Brazil 2014

Jaridun Brazil sun gode wa Alkalin wasa

Jaridun kasar Brazil a yau Juma’a sun yaba wa ‘Yan wasan kasar da suka fitar da kasar kunya a tashin farko, bayan sun doke Croatia ci 3-1. A cikin sharhin jaridun na Brazil wata Jaridar ma har da godiya ta yi wa alkalin wasa dan kasar Japan da ya ba kasar Fanalti.

Neymar na Brazil yana murnar zira kwallo a raga.
Neymar na Brazil yana murnar zira kwallo a raga. REUTERS/Ivan Alvarado
Talla

Croatia ce ta fara jefa kwallo a raga kafin daga bisani Neymar ya farke kwallon.

Jaridar Lance ta wasanni da ake bugawa a kowace safiya a kasar, a cikin sharhinta tace , “Kofinmu ne, Naymar namu ne kuma Oscar namu ne haka ma kwallon da Croatia ta jefa namu ne, kamar yadda alkalin wasa ya kasance namu, don haka komi na Brazil ne a karawar farko”

Naymar na Brazil yana Murnar jefa kwallo a raga.
Naymar na Brazil yana Murnar jefa kwallo a raga. REUTERS/Ueslei Marcelino

Jaridar Globo kuma ta maka babban labari ne mai taken “Arigato” Mun gode da harshen Japan, tana arashi ga Alkalin wasa.

Wasu jaridun kasar dai da dama sun lallashi al’ummar kasar su kwantar da hankali tare da ba ‘Yan wasa goyon baya domin fitar da kasar kunya a wannan gasa mai dimbin tarihi a duniya.

Cece kuce

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta kare alkalin wasa Yuichi Nishimura dan kasar Japan wanda ya ba Brazil Fanalti.

Matakin bayar da fanaltin ya janyo cece kuce, kuma hukuma FIFA ba ta bayyana cewa ko alkalin wasan zai sake yin alkalanci a wasu wasanni na gaba ba.

Shugaban alkalan wasa na hukumar FIFA, Massimo Busacca yace alkalin wasan ya yi daidai saboda dan wasan Croatia Dejan Lovren da gangan ya ture Fred na Brazil.

Amma wasu suna ganin sabanin haka, musamman mutanen Croatia suna ganin da gangan ne dan wasan ya harde kafa ya fadi.

Yanzu haka FIFA tace zata yi nazarin alkalancin mutumin na Japan domin tantance ko zai sake yin alkalanci a wasanni na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.