Isa ga babban shafi
Brazil 2014

An fara wasannin cin kofin duniya a kasar Brazil

Jiya Alhamis aka fara wasannin gasar cin kofin duniya, da za a yi a kasar Bazil, inda Brazil mai masukin baki ta kara da Croatia a wasan farko, da a suka yi a birnin sao Paulo. Shagulgulan da suka biyo bayan nasarar da Brazil ta samu kan Croatia, sun kawar da tashe tashen hankulan da aka gani a wasu sassan kasar, a kwanakin baya, don jama’a sun yi ta raye raye, da harba abubuwan wasan wuta a birnin Sao Paulo, bayan wasan.Sai dai fa dama cikin ‘yan kasar ta Croatia ya duri ruwa, don kuwa akasarinsu sun yi tunanin ‘yan wasan nasu zasu sha kashi.Yau juma’a kuma kasshen Spain da Netherlands, da suka buga wasan karshe a gasar cin kofin duniya da aka yi a Africa ta Kudu a shekarar 2010, zasu kara a birnin Salvador.A wani bangaren kuma, kungiyar taraiyyar Turai ta EU ta kaddamar da wani gangamin da ke yaki da aikata masha’a da yara kanana, yayin wasan na cin kofin duniya, kuma tuni ‘yan wasan kasar ta Brazil kamar su Kaka da Juninho Pernambucano, suka amince su bayar da goyon baya a wannan gangamin.Dama hukumomin kasar ta Brazil suna ta fargabar cewa wasu masu sha’awar wasan kwallon kafa daza su je kasar, zasu kuma nemi jin yadda harkar nishadi da ake ta dangantawa da kasar, take gudana. 

'Yan wasan Brazil suna murnar samun nasara a wasan su da Croatia
'Yan wasan Brazil suna murnar samun nasara a wasan su da Croatia 路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.